<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Akwai littafi a sama
 Wanda Allah ya yi
 Inda an sa sunayen duk masu bi.
 In babu sunanka
 A littafin nan
 Ba za a karɓe ka wurin Mai Tsarki can.

[V2]
 KORUS
 An sa sunana can
 Cikin Littafin Rai
 Tun da na karɓi Yesu
 An sa sunana can.

[V3]
 2) Da na zamna a duhu
 Ban san haryarsa ba
 Sai an ba ni labarin Yesu Mai Cetona
 Sai na tuba, na bi shi
 Na bar duk laifina
 Shi kuwa ya sa sunana a Littafinsa can.</lyrics>
<title>Akwai Littafi A Sama LW357</title>
<hymn_number>357</hymn_number>
</song>